Shekara 60 Sasamo Yancin Nigeria.

 Bayan shafe shekaru a ƙarƙashin mulkin mallakar Turawan Burtaniya, Fira Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa ya jagoranci ƙarbar ƴancin ƙasar sannan ya shugabanci gwamnatin gamayyar jam'iyyun da suka lashe zaɓen ƙasar.



An shafe makonni ana murnar hakan a wasu sassan ƙasar, sannan abu ne da ba zai taɓa gushewa a zuƙatan waɗanda suka halarci bikin ba a Filin Sukuwa, da a yanzu ya koma Dandalin Tafawa Balewa da ke Obalende a Lagos, ranar 1 ga watan Oktoban 1960.


''Kafin dare ya yi tsaka, sai aka kashe fitilu aka kuma sassauta tutar Burtaniya,'' kamar yadda Ben Iruemiobe ya shaida wa BBC, wani matashi da a loakcin yake da shekara 16, wanda ya shaidi yadda aka ɗaga tutar Najeriya.


''''Can kuma da tsakar dare sai aka kunna fitilun ta yadda suka haska tutar mai launin kore da fari da kore da ke tsaye ƙyam, ta yadda kowa zai iya gani. Bayan hakan sai kuma aka fara wasan tartsatsin wuta, sai kuma masu kiɗan soji suka fara nasu wasan inda muka nishaɗantu


Shekara bakwai bayan samun ƴancin kai, sai yaƙin basasa ya ɓarke a yankin gabashin Najeriya a ƙoƙarin ɓallewar jihar Biafra.


A ƙarshe ƴan Biafra sun miƙa wuya a yaƙin, wanda aka shafe shekara uku ana yi, ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum miliyan biyu, waɗanda da yawansu mata da yara ne waɗanda suka mutu saboda yunwa a gabashin Najeriyar.


Wani marubuci mazaunin Amurka Okey Ndibe, wanda yake yaro a lokacin yaƙin, ya bayyana lamarin da cewa mai matuƙar wahala ne a tarihin Najeriya.


''Babban burin gwamnati ya cika, amma fa hakan ya faru ne bayan da mutane da dama suka rasa rayukansu.


''Har yanzu yaƙin Biafra bai bar yi wa ƴan Najeriya gizo ba. Ƙaruwar rikici a yankin arewa maso gabas, sake farfaɗo da fafutukar Biafra, da kuma buƙatun ƴan yankin Naija Delta kan yin iko da albarkatun ƙasa, na daga cikin abubuwan da gazawar Najeriya wajen yin adalci ga tsare-tsaren al'umma ta jawo,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.


Source BBC Hausa.

No comments:

Post a Comment

Adbox