Auren Dan Atiku Da Yar Ribadu's (PDP vs APC) Da Zaayi.

 Shekaru da dama da suka wuce, Nuhu Ribadu ne shugaban hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati EFCC, yayin da Atiku Abubakar yake matsayin mataimakin shugaban Najeriyar a lokacin.



A yau mutanen biyu na son zama surukan jina. Ga abin da muka sani zuwa yanzu kan lamarin.


Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa Fatima Ribadu, ƴa ga Nuhu Ribadu, tsohon shugaban EFCC, za ta auri ɗan tsohon mataimakin Najeriya Aliyu Atiku Abubakar 


Rahotanni sun ce za a yi auren ne ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban 2020, kamar yadda aka wallafa a katin bikin, wanda BBC ta gani.



Sai dai daga Fatima Ribadu har Aliyu Atiku, babu wanda ya ce komai kan lamarin har zuwa yanzu.


Aliyu Atiku Abubakar, shi ne Turakin Adamawa, inda ya gaji babansa Atiku ɗan takarar shugaban ƙasar ƙarƙashin jam'iyyar PDP, bayan da ya zama Wazirin Adamawa a shekarar 2017.


Turakin Adamawa na ɗaya daga cikin muhimman muƙaman sarauta a Masarautar Yola.



Aliyu kuma ma'aikacin banki ne sannan daraktan kamfanin Priam Group, ɗaya daga cikin kamfanonin babansa. Yana kuma son ya gaji babansa ta fuskar siyasa.



Fatima Ribadu, ɗaya daga cikin ƴaƴan Nuhu Ribadu ce, tsohon shugaban hukumar EFCC.


Kuma babbar ƙawa ce ga ƴar Shugaba Muhammahu Buhari, Hanan.


A watan Disamban 2016, Hanan wacce ta ƙware a ɗaukar hoto, ta wallafa hotunan Fatima Ribadu a shafinta na Instagram.


Ƴan Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta kan auren manyan ƴan siyasar biyu daga jam'iyyu daban-daban masu adawa da juna.


Atiku Abubakar ɗan jam'iyyar PDP ne, yayin da Nuhu Ribadu yake ɗan APC.


Sai dai dukkan su ƴan asalin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ne




No comments:

Post a Comment

Adbox