JaWabin Shugaba Buhari Na Cika Shekara 60 Dasamun Yanci A Talabijin Zayyi

 Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai yi jawabi ga 'yan Najeriya ta talabijin a maimakon Dandalin Eagle wanda aka yi niyyar yi a baya.



A wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Femi Adesina ya fitar, ya bayyana cewa shugaban zai yi jawabin ne da misalin 7:00 na safe a ranar 1 ga watan Oktoba.


A sabuwar sanarwar, ya ce 'yan Najeriya su yi watsi da sanarwar baya da ta ce shugaban zai yi jawabin a gaban jama'a a Dandalin Eagle.


Ya kuma ce daga nan shugaban zai wuce Dandalin Eagle wurin taron cika ƙasar shekara 60 da samun 'yancin kai.





No comments:

Post a Comment

Adbox