Wasu Daga Cikin Jaruman Kannywood Dasukayi Murnan Samun Yanci.

 Ali Nuhu wanda aka fi kira da Sarkin Kannywood, ya wallafa wannan hoton tare da cewa: ''Ƴancin kai da ƴanci na gaskiya kan samu ne kawai ta hanyar yin abin da ya dace. A matsayinmu na ƴan Najeriya, ƙasarmu da muke ƙauna, muna buƙatar yin abin da ya dace don ganin sauyin da ko yaushe muke magana a kansa ya samu. Ƙasarmu ta cika shekara 60, dole mu yi fafutuka a tare don tabbatar da martabarta.''





Fati Washa kuwa cewa ta yi: ''Ku zo mu ɗaga hannu don murnar wannan ranar tare da yin bikinta. Ku zo mu tashi tsaye don nuna girmamawarmu ga jagororin da suka mutu a fafutukar nemo mana ƴanci. Ku zo mu rera taken ƙasarmu ɗauke da tutoci a hannayenmu don bikin wannan rana mai muhimmanci.''



Shi ma tauraro Sani Danja ya wallafa wannan hoton ne tare da wasu yara inda ya ce: ''Yaranmu na yau, shugabannin gagarumar ƙasarmu Najeriya. Barka da zagayowar ranar samun ƴancin kai Najeriya.''




Sannan Shima Sadiq Sani Sadiq Yana murnan shekara 60 Dasamun yancin kasarnan.




Sannan akwai Maryam Yahaya jaruma Wanda itama tana murna saboda samun yancin kasarnan.



No comments:

Post a Comment

Adbox