An Haramta Wa SARS Tare Hanyan Wucewa

 Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya haramta wa runduna ta musamman mai yaƙi da fashi da makami da ake kira SARS da sauran ɓangarorin rudunonin ƴan sanda kafa shingayen bincike.



Cikin sanarwar da shafin Twitter na rundunar ƴan sandan Najeriya ya wallafa a wasu jerin saƙwanni ranar Lahadi, sufeton ƴan sandan ya haramta wa dukkanin rundunoni na musamman da suka haɗa da FSARS da STS da IRT da ke yaƙi da ƙungiyoyin asiri kafa shingayen bincike domin tarewa da binciken ababen hawa.


Sannan an haramta wa duk wani jami'in ƴan sanda fitowa da kayan gida ba tare da kayan ƴan sanda ba. Sanarwar ta ce wasu jami'an na fakewa da wannan suna yin abubuwan da ba su dace ba da suka saɓa doka.



Babban Sufeton ƴan sandan ya kuma yi gargaɗi ga rundunonin game shiga haƙƙin sirrin rayuwar mutane musamman bincike wayoyinsu na salula da kwanfuta da sauran na'urori ba tare da wani samun izini ba.


Sanarwar ta ce an kama wasu daga cikin jami'an SARS da ake zargi da cin zarafin mutane a Legas, sannan za a ci gaba da bincike kan zargin cin zarafi da wasu jami'an rundunar SARS suka aikata.


An buƙaci jami'an su mayar da hankali ga laifukan da suka shafi fashi da makami da satar mutane da sauran muggan laifukan da aka kafa rundunonin domin su, ba su koma cin zarafin al'umma ba.


No comments:

Post a Comment

Adbox