SARS : Yan Sanda Da Yan Twitter

 Mabiya shafukan sada zumunta na Tuwita a Najeriya sun yi wa ƴan sandan ƙasar ca, musamman ma na rundunar nan ta musamman mai yaƙi da fashi da makami da ake kira SARS.



Hakan ya biyo bayan mutuwar wani matashi ne da ake zargin ƴan sandan ne sanadi wanda suke zargin sa da kasancewa ''ɗan damfara'' da aka fi sani da ''Yahoo Boys'' a Osogbo, babban birnin Jihar Osun.


Rahotanni sun ce ƴan sanda sun bi matashin tare da wasu matasan uku a mota, inda a ƙoƙarinsu na tsere wa ƴan sandan suka yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar yaron a ranar Talata da yamma.


Matashin mai suna Remi a take yanke ya mutu, yayin da aka garzaya da sauran ukun da suka jikkata asibiti.


Tuni dai mazauna birnin suka ce matasa sun fara zanga-zangar nuna taƙaicinsu kan lamarin.


Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mai magan da yawun ƴan sandan jihar Yemisi Opalola ta ce: ''Lamarin ya faru amma muna iya bakin ƙoƙarinmu don shawo kansa.''


No comments:

Post a Comment

Adbox