Wasu Jahohin Sunbude Mukarantu.

 Kaman yadda shugaban kasa yafadi ankusan bude makarantu to yanxun haka wasu sunriga Sunbude nasu.




Bayan kwashe sama da wata shida sakamakon cutar korona, wasu jihohin Najeriya za su buɗe azuzuwa a yau don ci gaba da karatu.


Jihohin Kebbi da Kwara da kuma Katsina,na daga cikin jihohin da zasu bude makarantun a yau don ci gaba da karatu.


Za a bude makarantun firamare da sakandire na gwamnati da kuma masu zaman kansu ne cikin tsauraran matakan kariya saboda cutar korona.


Kwamishinan ilimi na jihar Katsina, Dakta Badamasi Lawal, ya shaida wa BBC cewa, an yi feshin kashe kwayoyin cututtuka a makarantu, sannan an tanadi wuraren wanke hannu, sannan kuma dole ne dalibai da malamai su rinka sanya takunkumin fuska.


Source BBC Hausa and 9ijastars.

No comments:

Post a Comment

Adbox