Yaune Sarki Yacika Kwana Bakwai Da Rasuwa Waye Kake Ganin Zaimaye Gurbinsa.

 A yau ne marigayi Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris ya ke cika kwana bakwai da rasuwa kuma ya rasu ne a wani asibiti da ke Kaduna.


Ya rasu yana da shekara 84 a duniya bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya. Marigayin dai ya shafe tsawon shekara 45 a kan karagar mulki.


A yanzu dai an samu wadanda suka suka ayyana ra’ayinsu na son maye gurbin marigayin sannan gwamnan Kaduna, Nasir El Rufa’I ya ce ya zuwa ranar Juma’a, mutum 11 ne suke son zama sarkin Zazzau.





Ya bayyana haka ne a yayin da yake karyata rahotannin wasu kafafen watsa labaran Najeriya da suka yi ikirarin cewa an mika masa sunayen mutum uku da ke son maye gurbin marigayi Alhaji Shehu Idris.


Wata sanarwa da kakakin gwamnan Muyiwa Adekeye ya fitar ranar Juma’a ta ambato sakataren gwamnatin jihar Kaduna Balarabe Abbas Lawal, yana cewa: “Tsarin zaben sabon sarkin Zazzau yana ci gaba cikin nutsuwa da taka-tsantsan saboda muhimmancin yanke hukunci” kan wannan babban lamari.


Gwamnan tun farko ya ce ya karanta wasu litattafai biyu da wasu turawa suka rubuta kan sarautar Zazzau kuma a halin da ake ciki ya shiga karanta littafi na uku domin su zame masa ja-gaba wajen fahimtar yadda zai bullowa batun nada sabon sarkin.


Source: BBC Hausa.

No comments:

Post a Comment

Adbox