Gwamna Bello Matawalle ya nemi matashin nan da yake tattaki daga wani yanki na jihar Kaduna zuwa Zamfara da ya koma inda ya fito.
Gwamnan ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.
Gwamnan dai ya shawarci matashin ya nemi wani abu mai muhimmanci ya yi a maimakon jefa kansa cikin kasada.
A cewar gwamnan, "a matsayina na uba, ina son na hana matasa jefa rayuwarsu cikin haɗari, a don haka nake fatan zai dakatar da tatakin tare da mayar da hankali kan wani abu da zai amfane shi."
Matashin na tattakin ne saboda so da ƙauna da yake yi wa gwamnan,
Wannan ba shi ne karo na farko da matasa ke yin tattaki ba ga shugabanninsu, inda ko a 2015 ma sai da wani matashi ya kwatanta yin haka bayan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ci zaɓe.
Hakazalika an samu wani matashin ma da ya yi tattakin zuwa Kano tun daga Katsina domin taya gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje murnar lashe zaɓe a 2019
No comments:
Post a Comment