Tsarin Neman Aure A Intanet

 

Duk wani namiji ko mace da ta kai wani munzali na manyance abu na farko da ake yi mata fata shi ne samun miji na gari.


Bisa al'adar ƙasar Hausa namiji ne yake ganin mace idan hankalinsa ya kwanta da ita sai ya tura iyaye ko manyansa a nema masa izinin har a kai matakin soma batun aure.



Ko da yake a wasu lokutan akwai auren haɗi da iyaye kan yi wa ƴaƴansu don ƙarfafa zumunci ko abota tsakanin iyalai biyu.


Amma kamar yadda Hausawa ke cewa duniya juyi-juyi, kusan a wannan lokaci zamani ya zo da abubuwa da dama inda a wasu lokuta ma mace ke iya ganin namiji ta furta hankalinta ya natsu da shi ko tana fatan ya aure ta.


No comments:

Post a Comment

Adbox