Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ya shiga littafi na uku kan tsarin zabar sabon sarki Zazzau.
Tun farko dai ya ce yana karance-karance ne domin su zame masa ja-gaba wajen fahimtar yadda zai bullowa batun nada sabon sarkin.
kuma bukaci jama'a da su ci gaba da taya shi addu'a domin yin zabe nagari Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya sake yin karin haske kan halin da ake ciki game da zabar sabon sarkin Zazzau.
El Rufai ya bayyana cewa a yanzu ya shiga cikin littafi na uku na karance-karancen yadda zai nada sabon sarki.
Gwamnan ya kuma roki jama’a da su ci aba da taya shi addu’ar Allah yayi masa jagora wajen zaba wa al’umman Zazzau sarkin da zai kawo cigabansu da masarautar Zazzau.
“Karin bayani kan Kaduna: Yayinda nake jiran rahoton ma’aikatar harkokin masarautu na jihar, ina cikin littafi na uku kuma na karshe kan tsarin zaben sabon sarki.
Za a turo mani shawarwarin ma’aikatar da tsaro kan yan takarar domin yanke hukuncin karshe.
“Littafin Dr Hamid Bobboyi kan manufofin shugabanci bisa ga tsarin magabata na masarautar Sokoto yana tattare da nasarori masu yawa.
No comments:
Post a Comment