Yadda Hauwa Ojeifo Tasami Kyauta Wajen Mai Kudin Duniya Bill Gate.


 

Hauwa Ojeifo, ta samu kyautar ne sakamakon gudumawar da take bayarwa wurin daidaiton jinsi bayan fuskantar cin zarafi ta da taba yi


Matar ta samu jinjinar Queen's Young Leaders sakamakon lura da kokarinta wurin jawo masu matsalar kwakwalwa a jikinta da kuma basu kwarin guiwa


Wata 'yar Najeriya mai suna Hauwa Ojeifo ta samu gagarumar kyauta ta musamman daga gidauniyar Bill Gates da Melinda Gates ta shekarar 2020.


Kasancewar budurwar mai rajin kare hakkin jinsi da nakasassu ce, tana jagorantar wata kungiya mai taimako da bada shawarwari ga masu fama da rashin lafiyar kwakwalwa.


Hauwa Ojeifo tana bawa masu damuwa karfin gwuiwa ne ta hanyar basu labarin rayuwarta da irin kalubalen da ta fuskanta.


Sannan sunbiya da hankalinta da kwazaonta irin jajircewanta akan taimakon datake yi har suka Bata Wannan kyautar.


No comments:

Post a Comment

Adbox