Abinda Yasa Zaayi Jirgin Kasa Daga Kano Zuwa Nijar - Garba Shehu.

 


Gwamnatin Najeriya ta ce ta amince da ƙudurin shimfiɗa layin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Katsina kuma ya dangana da jamhuriyar Nijar domin bunƙasa safarar kayayyaki.


Bayanai sun ambato cewa aikin zai laƙume kuɗi har dala biliyan 1 da miliyan 96.


Sabuwar kwangilar shimfiɗa layin dogon na zuwa daidai lokacin da Najeriya ke kukan ƙarancin kuɗaɗen shiga sakamakon raguwar kuɗin da ƙasar ke samu daga cinikin man fetur.


Mai ba da shawara na musamman ga shugaban Najeriya kan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC Hausa ce gwamnati za ta ciyo bashi don yin aikin, la'akari da cewa jirgin ƙasar zai mai da kuɗinsa nan gaba.


Ya ce titin jirgin zai tashi daga Kano ya ratsa jihohin Katsina da Jigawa ya kuma kare a cikin Jamhuriyar Nijar.


Kakakin shugaban kasar ya ce ana sa ran soma aikin a watan gobe.


A cewar Garba Shehu samar da jirgin kasar zai zama babbar nasara ga kasashen Najeriya da Nijar ta fuskar kasuwanci.


No comments:

Post a Comment

Adbox