A Duk Lokacinda Dayayi Min Fyade Yana Bani Giya Inji Wata Mata.

A duk lokacin da ya yi min fyaden, yana bani magani da giya saboda kada in dauka ciki. Ubangidana yana barazanar kasheni idan na sanar wa wani. 'Yan sanda sun kama shi kuma na basu maganin da yake bani," Balogun tace.


Kamar yadda rahoton ya bayyana, an mika wa 'yan sanda koken kuma sun kama shi, amma babu dadewa suka sakesa ba tare da gurfanar da shi ba.




Balogun, wacce 'yar asalin Abeokuta ce daga jihar Ogun, ta je aiki a jihar Legas don samun abinda za ta taimaki rayuwarta da shi.


Wannan Karan yakamata gwamnati ta duba a ladabtar dashi ko Dan yazama gargadi ga masu aikatawa da masu niyyan yin haka.

Ta ce tana bukatar a yi mata adalci a kan abunda yayi Mata.


No comments:

Post a Comment

Adbox