Tsofaffin Jiga Jigan Sarakunan Arewacin Nijeriya.



Yayin da ake ci gaba da jimamin rasuwar sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris wanda ya rasu ranar 20 ga watan Satumbar 2020, Aka Duba da waiwaye kan wasu daga cikin manyan sarakunan arewacin Najeriya da suka rasu a kan mulki.


A lokacin da suke raye, wadannan sarakunan kusan sa'o'in juna ne kuma wasu daga cikinsu sun yi zamani tare.


Haka kuma, akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin waɗannan masarautun na arewacin Najeriya



Sarkin Musulmi Muhammadu MacciÉ—o Abubakar



Muhammadu Maccido Abubakar shi ne Sarkin Musulmi na 19 a Najeriya


An haifi Muhammadu MacciÉ—o Abubakar ne ranar 20 ga watan Afrilu 1926 a jihar Sokoto a Najeriya.


Mahaifinsa Siddiq Abubakar III ya yi Sarkin Musulmi a Najeriya tsawon shekara 50 kafin rasuwarsa a 1988, inda Ibrahim Dasuki ya maye gurbinsa.


MacciÉ—o ya hau karagar mulki ne yana da shekaru 70 a shekarar 1996 bayan da gwamnatin tsohon shugaban mulkin soja Sani Abacha ta cire Ibrahim Dasuki daga matsayinsa na Sarkin Musulmi.


Sarki Muhammadu MacciÉ—o shi ne Sarkin Musulmi na 19 a kasar.


Ya rasu a hatsarin jirgin sama na ADC wabda ya tashi daga Abuja zai tafi Sakkwato ranar 28 ga watan Oktobar 2006.


An naÉ—a Sarki Muhammadu Sa'ad Abubakar a matsayin sabon Sarkin Musulmi kuma magajin MacciÉ—o ranar 2 ga watan Nuwamba 2006.




Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero





Ado Bayero shi ne sarkin mafi dadewa a sarakunan Fulani a kano


An haifi marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero a watan Yuli na shekarar 1930.


Mahaifinsa shi ne Alhaji Abdullahi Bayero wanda ya yi sarautar Kano tsawon shekaru 27.


A ranar Juma'a 11 ga watan Oktobar 1963 ne kuma aka naÉ—a Alhaji Ado Bayero a matsayin sarkin Kano bayan rasuwar Sarki Muhammad Inuwa É—an Sarki Abbas.


Ya hau sarautar Kano yana da shekaru 33, sannan ya yi mulki na tsawon shekaru 51.


Alhaji Ado Bayero shi ne sarkin mafi daÉ—ewa a sarakunan Fulani a Kano da suka fara mulki bayan jihadi a shekara ta 1807.


Marigayin Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya rasu ranar 6 ga watan Yunin 2014 yana da shekaru 84 a duniya, ya kuma bar mata huÉ—u da 'ya 'ya sama da 60 da jikoki fiye da 300.


An naÉ—a Muhammadu Sanusi II a matsayin magajin Ado Bayero ranar 8 ga watan Yunin 2014.


Sarkin Katsina Dakta Muhammadu Kabir Usman




Sarki Muhammadu Kabir shi ne sarkin Fulani na 10 a Katsina


An haifi Dakta Muhammadu Kabir Usman a shekarar 1928.


Ya gaji mahaifinsa Usman Nagogo wanda ya yi mulkin Katsina daga shekarar 1944 zuwa rasuwarsa a 1981.


Sarki Muhammadu Kabir shi ne Sarkin Fulani na 10 a Katsina kuma sarki na 3 daga gidan Sulluɓawa.


A lokacin mulkinsa ne aka ƙirƙiri jihar Katsina daga jihar Kaduna.


Muhammadu Kabir ya rasu ran 8 ga watan Maris É—in 2008 yana da shekara 80. Ya rasu ya bar mata uku da yara da dama.


An naÉ—a É—ansa Abdulmumini a matsayin sabon sarki kuma magajinsa ran 13 ga watan Maris 2008.




Sarkin Daura Muhammadu Bashar




An haifi Muhammadu Bashar a shekarar 1926 a garin Daura, kuma asalinsa É—an gidan sarauta ne.


Kakansa Malam AbdulRahman Musa shi ne Sarkin Daura na 58 kuma ya yi mulkin kasar tsawon shekaru inda bayan rasuwarsa ne Muhammadu Bashar ya gaje shi a watan Yunin 1966.


Muhammadu Bashar shi ne Sarkin Daura na 59.


Ya rasu ranar 25 ga watan Fabrairun 2007 bayan shekara 41 a kan karagar mulki.


An naÉ—a Sarki Umar Farouk a matsayin sabon Sarki ranar 28 ga watan Fabrairun 2007.



Sarkin Gombe Shehu Usman Abubakar




Sarki Shehu Usman Abubakar shi ne Sarkin Gombe na 10 kuma ya yi mulki ne daga Janairun 1984 zuwa watan Mayun 2014 a lokacin rasuwarsa.


Ya rasu ne ranar 27 ga watan Mayun 2014.


Kafin ya zamo sarki a cikin watan Janairun 1984, Marigayi Alhaji Shehu Usman Abubakar ya yi aikin gwamnati a matakai daban-daban.


Ya rasu yana da shekara 76 da haihuwa, kuma ya shafe kimanin shekara 30 a kan gadon sarauta a matsayin Sarkin Gombe na goma, bayan ya gaji mahaifinsa Abubakar Umar Farouk.



LamiÉ—on Adamawa Dakta Aliyu Mustapha



An haifi Dakta Aliyu Mustapha ne a 1922, an kuma naÉ—a shi LamiÉ—on Adamawa na 11 ranar 26 ga watan Yuli 1953.


Ya karɓi sandar mulki daga hannun Gwamna Sir Bryan Sherwood-Smith, zamanin Turawan mulkin mallaka.


Don haka Dakta Aliyu Mustapha ya shafe shekara kusan 57 a kan karagar mulki.


Tsatso ne na Lamiɗon Adamawa na farko, Lamiɗo Adama, wanda shi kuma ya karɓi tutar jihadi daga mujaddadi, Shehu Usman Dan Fodiyo.


LamiÉ—o Aliyu Mustapha ya rasu ne ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2010 yana da shekaru 88 a duniya bayan kwashe shekaru 57 yana mulki.


ÆŠansa Muhammadu BarkinÉ—o ne ya gaje shi inda aka naÉ—a shi LamiÉ—on Adamawa ranar 18 ga watan Maris É—in 2010.


Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris



Alhaji Dakta Shehu Idris shi ne sarkin da ya fi ko wanne dadewa a karagar mulki a cikin sarakunan Zazzau


An haifi Alhaji Dakta Shehu Idris ne a watan Maris na shekarar 1936.


Sunan mahaifinsa Idrisu amma an fi saninsa da Auta.


An ba shi sarautar Sarkin Zazzau ne ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar 1975 bayan rasuwar Sarki Muhammadu Aminu.


Sarki Shehu Idris shi ne Sarkin Zazzau na 18 kuma wanda ya fi ko wanne a sarakunan Zazzau daÉ—ewa a kujerar mulki.


Ya rasu ranar 20 ga watan Satumbar 2020 yana da shekaru 84.


No comments:

Post a Comment

Adbox