Commander Yan Sanda na Accra wato Ghana ya nemi Yan Sanda Dasu Rage yawan Jima'i don Zabe.
Wato abunda yaje nufi cewa Yana ragema Yan Sandan karfi ne.
Rundunar ƴan sandan Ghana ta bukaci jami'anta su rage yawan jima'i domin samn karfin da za su tunkari hayaniyar babban zaɓen kasar da za a gudanar a watan Disamba mai zuwa.
Kwamandan ƴan sandan yankin Accra na rundunar ƴan sandan, DCOP Afful Boakye-Yiadom ya ce kiran ya zama wajibi saboda yawan jima'i yana rage ƙarfi, kuma hakan zai yi tasiri a yunƙurin tabbatar da zaman lafiya lokacin zaɓe.
"Ku rage yawan jima'i, muna buƙatar ƙwazo a lokacin zaɓe, don haka ina ba ku shawara ku rika cin abinci sosai, ku rage yawan jima'i domin ku samu ƙarfin da za ku iya aiki a lokaci da kuma bayan zaɓen 2020", a cewar DCOP Afful Boakye-Yiadom.
No comments:
Post a Comment