Tarwatsen Da Akayi Wa Masu Zanga Zanga A Abuja.

 Yan sandan Najeriya sun harba hayaƙi mai sa ƙwalla kan masu zanga-zangar da ke son a soke rundunar SARS da ke yaƙi da 'yan fashi da makami a Abuja babban birnin ƙasar.



Suna zanga-zangar ce bayan wani bidiyo ya karaɗe shafukan intanet inda ya nuna yadda wasu da ake zargi jami'an SARS ne sun kashe wani mutum.


An gudanar da jerin irin wannan zanga-zanga a birane da dama na ƙasar, ciki har da Lagos. Taurarin fina-finai irin su John Boyega da Mr Macaroni na cikin waɗanda suka halarci zanga-zangar.


Tun da farko masu zanga-zangar sun nuna matuƙar rashin jin daɗinsu kan jami'an rundunar Special Anti-Robbery Squad (Sars), wadda ake zargi da azabtar da mutane da kisan kai.


SARS: Shin da gaske gwamnati take kan batun sauya fasalin ƴan sandan SARS?


Police Reform: Mece ce dokar sauya fasalin aikin ƴan sandan Najeriya?


'Yan ƙasar suna amfani da maudu'in #EndSARS a dandalin Twitter bayan fitowar bidiyon da ake zargi jami'an rundunar SARS sun kashe wani matashi ranar Asabar da ta wuce.


Mutane da dama kuma suna amfani da maudu'in domin jan hankali kan musgunawar da 'yan sandan ƙasar suke yi musu.


Ranar Lahadi babban sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya haramta wa rundunar ta Sars tsare mutane a shingayen duba ababen hawa da kuma sanya shingayen.


Ya kuma ce dole jami'an Sars su riƙa sanya kayan aikinsu wato uniforms sannan ya yi alƙawarin gudanar da bincike kan abin da ya faru


Sai dai masu zanga-zangar sun nace cewa dole a soke rundunar baki ɗaya kowa ya huta.


No comments:

Post a Comment

Adbox