Shirin Dadin Kowa : Bayanai Da Nishadartarwa.

 Fim mai dogon zango sabon al'amari ne a harkar fina-finan Hausa, waɗanda galibi ake shiryawa a arewacin Najeriya.



Wannan nau'in fim ya ƙunshi labari mai tsayi sosai, saɓanin irin waɗanda aka saba gani a masana'antar Kannywood - wato gajerun fina-finai da akan iya kalla a lokaci guda su ƙare.


Galibin fim mai dogon zango yana da jigogi manya da ƙanana.


Daɗin Kowa yana ɗaya daga cikin fina-finan Hausa masu dogon zango na farko-farko.


Hasali ma, zan iya cewa, shi ne fim ɗin Hausa mai dogon zango mafi shahara da karɓuwa a wajen mutane kawo yanzu - musamman a baya-baya nan.


Fim ne mai cike da abubuwan barkwanci, da ban tausayi, da ban haushi da kuma darussa kan zamantakewar al'umma.


Wannan fim, ana nuna shi a tashar talabijin ta Arewa24, kuma a halin da ake ciki, ana cikin zango na uku mai taken: "Wasa Farin Girki".


Wannan ya biyo bayan "Daɗin Kowa" zangon farko da kuma "Sabon Salo"


No comments:

Post a Comment

Adbox