Wuka Da Nama Na Hannun Malam Nasiru El Rufai Kan Nadin Sabon Sarkin Zazzau.

 yayin da Yan Najeriya musamman mutanen da ke masarautar Zazzau ke jiran a nada musu sabon sarki, hankulansu sun karkata kan Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna, wanda wuka da nama ke hannunsa kan batun.


A ranar Lahadi Sarki Alhaji Shehu Idris ya rasu a wani asibiti da ke Kaduna bayan fama da gajeriyar rashin lafiya yanada shekara 84 ya rasu.


Kamar kowacce sarauta mai muhimmanci, tuni masu son maye gurbinsa suka ayyana ra’ayinsu kuma gwamnan da kansa ya ce ya zuwa ranar Juma’a, mutum 11 ne suke son zama sarkin Zazzau.


Ya bayyana haka ne a yayin da yake karyata rahotannin wasu kafafen watsa labaran Najeriya da suka yi ikirarin cewa an mika masa sunayen mutum uku da ke son maye gurbin marigayi Alhaji Shehu Idris.


Wata sanarwa da kakakin gwamnan Muyiwa Adekeye ya fitar ranar Juma’a ta ambato sakataren gwamnatin jihar Kaduna Balarabe Abbas Lawal, yana cewa: “Tsarin zaben sabon sarkin Zazzau yana ci gaba cikin nutsuwa da taka-tsantsan saboda muhimmancin yanke hukunci” kan wannan babban lamari.


Gwamnan ya ce Yana karanta littafai biyu da wasu turawa suka rubuta kan sarautar Zazzau. 



Domin su zame masa ja-gaba wajen fahimtar yadda zai bullowa batun nada sabon sarkin.


A al'adance dai akwai hanyoyi da Dana da ake laakari da su wurin zaben sarki



A yayin da Gwamna El-Rufai ke ci gaba da karatu, ‘yan Najeriya kuma na ci gaba da zuba ido domin ganin ranar da za a nada sabon sarkin Zazzau.





No comments:

Post a Comment

Adbox