Sama Da Miliyan Talatin (30) Sun Bata Inji Hukumar Kano.


 

Hukumar da ke karbar korafe-korafe ta jahar Kano ta ce ta samu labarin badakalar wasu kudade sama da naira milliyan 30 da aka yi sama da fadi da su a ma'aikatar noma ta jihar.


Hukumar ta ce ta gano batan kudaden ne biyo bayan wani koke da ta samu daga wata kungiya ta mata manoma.


Shugaban hukumar karbar korafe-korafen al'umma Muhuyi Magaji Rimin Gado ya fadawa BBC cewa ma'aikatar na karbar kudade daga masu amfani da kadarorin gwamnati kamar gonaki da sauransu, to amma kudin ba ya shiga asusun gwamnati.


Ya ce sun samu bayanai ne daga kungiyoyin manoma da su ka hada da kungiyar mata manoma ta jihar Kano.


Acewar Muhuyi Magaji daga bayanan da suka samu suna zargin ''an karbi akalla naira miliyan 30 da wani abu.Kuma tun ba a je banki ba masu bincike sun samu tsabar kudi a ma'aikatar da ya kai naira miliyan bakwai da wani abu.''


Jami'in ya bayyana cewa babban wnda su ke zargi a badakalar shine babban sakataren ma'aikatar gona, don a cewarsa shi ke da ruwa da tsaki wurin karbar kudaden kamar yadda bincike ya nuna.


To amma a kafafen sada zumunta da dama na yada cewa tuni hukumar na kan binciken mataimakin gwamnan jahar Dr Nasiru Yusuf Gawuna kan hannu a badakalar, duk da shugaban hukumar ya ce sam wannan ba gaskiya bane.


Hasali ma ya ce mataimakin gwamnan ne ke ba su goyon baya a binciken da suke yi, ganin cewa ma'aikatar gonar a karkashin ofis dinsa ta ke


No comments:

Post a Comment

Adbox