ENT: Mutane Hudu (4) Dazasu Iya Yin Sarautan Garin Zazzau.

 


Wainnan sune mutane hudu (4) Dazasu iya yin Sarautan Garin Zazzau.

1 : Turakin Zazzau - Aminu Shehu Idris


2 : Magajin Garin Zazzau - Ahmad Nuhu Bamalli


3 : Iyan Zazzau - Bashir Aminu


4 : Galadiman Ruwan Zazzau - Mannir Jaafaru


Yayin da ake zaman makokin rasuwar Sarkin Zazzau mai martaba Alhaji Shehu Idris, yanzu hankalin ƴan Najeriya musamman arewacin ƙasar ya karkata ne ga abon sarkin da zai gaje shi.

A ranar Lahadi ne Allah Ya yi wa mai Martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa bayan shafe shekaru 45 kan gadon sarautar Zazzau.

Marigayin wanda shi ne sarkin Zazzau na 18, ya rasu ne yana da shekara 85 a duniya.

Bisa tsarin sarautar Zazzau ana zaɓen sabon sarki ne daga gidajen masarautar guda huɗu - wato daga Gidan Mallawa da Gidan Barebari da Gidan Katsinawa da kuma Gidan Sulluɓawa.

Masanin tarihin masarautar Zazzau kuma daraktan gidan Tarihi na Arewa da ke ƙarƙashin Jami'ar Ahmadu Bello, Shu'aibu Shehu Aliyu ya shaida wa BBC cewa waɗannan gidajen ne ke turo ɗan takara ɗaya da zai nemi sarautar Zazzau ga masu zaɓen sabon sarki.

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ne zai zaɓi sabon Sarkin Zazzau, cikin mutum uku daga cikin ƴaƴan gidan masarautar Zazzau da masu naɗin sabon sarki suka tura masa.

No comments:

Post a Comment

Adbox