Babban Siniman Da Gwamnan Jihar Kaduna Zai Ginama Yan Kannywood.


 

Babban Siniman Da Gwamnan Jahar Kaduna Zai Ginama Yan Kannywood



Gwamnan ya ba su fili mai fadin murabba'i dubu 8000 domin gina babbar sinima ta zamani, da kuma gudunmawar kudin, a cewar wani fitaccen tauraro na Kannywood, Malam Falalu Dorayi babban directa.


A cewarsa, masu ruwa da tsaki na Kannywood karkasin wata kungiya da ake kira Movie Hope ne suka nemi gwamna ya ba su filin da za su gina katafariyar sinima wadda a cikinta za a iya daukar fina-finai sannan a nuna su.


Kuma Jaruman kannywood Sunyi Alfahari da jin Dadi akan abunda shi Gwamna Mal. Nasiru yayi musu.


"Da ma an dade da kai masa kuka cewa akwai bukatar a samu fili a Kaduna wanda za a gina sinima, kamar yadda aka bukaci wasu gwamnoni su ma su yi a jihohinsu. Ginin zai kunshi sinima da wurin koyon sana'o'i da wurin yin daukar muryar mawaka da kuma sutudiyo, da wuraren cin abinci da wuraren shakatawa," in ji Falalu Dorayi.


No comments:

Post a Comment

Adbox