Anci Tarar Sanatan Nijeriya Naira Miliyan 50 Kan Cin Zarafin Wata Yarinya.

 An ci tarar wani Sanatan Najeriya naira miliyan 50 da kuma neman afuwan wata mata da ya ci zarafinta a shagon sayar da kayan jima'i a shekarar da ta gabata.


Wata babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta ce abin da Sanata Elisha Abbo ya aikata "rashin imani ne da kaskantarwa" da karya ka'idojin hakkin bil adama.





Cin zarafin da aka nada a hoton bidiyo kuma aka ta yada wa a intanet, ya nuna yadda Mr Abbo ya mari Ms Warmate.


Bayan shan caccaka da zanga-zanga kan abin da Sanatan ya aikata, daga baya ya fito fili ya nemi afuwa, amma duk da hakan Ms Warmate ta shigar da kara a gaban kotu,


Baya ga biyan wannan tara, kotun ta kuma bukaci shi ya rubuta wasikar nemi afuwa a jaridun kasar.


Kungiyoyin kare hakkin mata sun yi murna da wannan hukunci.


Ko da yake, lauyoyin Mr Abbo sun shaida wa BBC cewa za su daukaka kara, kuma suna da damar kwanaki 90.


Labarai Daga BBC Hausa.

No comments:

Post a Comment

Adbox